<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>130</hymn_number>
<title>Ran da Ubangiji Za Ya Dawo LW130</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ran da Ubangiji za ya dawo
 Don ya karƃi Masu Bi,
 Ko za ya iske ka kana tsaro?
 Ko fitilarka 'na ci?

[V2]
 KORUS
 Sai dai ka tabbata ka yi shiri
 Ko an kira ka yanzu,
 Domin ka sadu da Ubangiji,
 Lalle, lalle ya fi kome kyau.

[V3]
 2) Ran da ya tafi, ya ba ka aiki
 Wanda za ka dinga yi.
 Ko ka yi aikinsa da aminci?
 Ko ka ƃata lokaci?
 Korus

[V4]
 3) Ran da ka mayai da talents naka,
 &quot;Bawan kirki,&quot; za ya ce?
 &quot;Shiga ka huta a cikin gida,&quot;
 Ko, &quot;Kai mugun bawa ne&quot;?
 Korus

[V5]
 4) Ba daman shiri idan ka mutu,
 Ba ka iya ruɗinsa.
 Kada ka kasa ka shige hutu
 Domin rashin gaskiya.
 Korus</lyrics>
</song>